in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Majalisar dokokin Birtaniya ta bukaci a gyara yarjejeniyar ficewar kasar daga EU
2019-01-30 13:37:36 cri
Majalisar wakilan kasar Birtaniya ta zartas da wani gyararren daftari game da yarjejeniyar ficewar kasar daga kungiyar tarayyar Turai EU a jiya Talata, inda ta bukaci firaministar kasar Teresa May da ta ci gaba da yin shawarwari tare da tarayyar Turai, da yin amfani da sabon shiri don maye gurbin abubuwan da suka shafi batun iyakar Ireland a cikin yarjejeniyar ficewar Birtaniya da aka cimma yanzu.

Gyararren daftarin, wanda ya bayyana matsayin da majalisar dokokin kasar ke da shi, ba shi da wani amfani ta fuskar doka, amma majalisar za ta iya yin amfani da shi wajen matsawa gwamnatin Birtaniya lamba. Teresa May ta ce, majalisar dokokin kasar ta bukaci a sake gyara yarjejeniyar ficewar Birtaniya daga EU, al'amari ne da ya danka mata izini wajen sake farfado da shawarwarin tare da EU, amma ba abu ne mai sauki ba.

Bisa yarjejeniyar, an ce, idan Birtaniya da EU sun kasa cimma matsaya daya kan wani shirin da ya shafi harkokin kasuwanci na yankin arewacin Ireland a yayin da Birtaniya take shirin ficewa daga EU, to, bayan da Birtaniyar ta gama shirin, za'a soma amfani da wani sabon shiri na daban. Masu sharhi kan al'amura sun ce, wannan sabon shiri na daban zai sa yankin arewacin Ireland ci gaba da mutunta ka'idojin kasuwancin tarayyar Turai, abun da zai sa arewacin Ireland zai ci gaba da kasancewa cikin tarayyar Turai.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China