Firaiministar Birtaniya ta fara tattaunawa kan sabuwar yarjejeniyar ficewa daga tarayyar Turai
A jiya Laraba, Firaiministar Birtaniya Theresa May ta samu gagarumin rinjaye a zaben da aka kada na kuri'ar yanke kauna a majalisar kasar, lamarin da ya kawar da duk wani yunkurin gaggauta babban zaben kasar wanda zai iya taimakawa jam'iyyar Labour.
Bayan fuskantar kalubale wanda zai iya sanadiyyar kwace ikon majalisar kolin ta Downing Street ta kasar, May ta sanar da cewa, za ta shirya wata ganawa da shugabannin jam'iyyun adawa domin yin watsi da sabuwar yarjejeniyar ficewar kasar daga tarayyar Turai. (Ahmad Fagam)