Tun a watan Disamban bara ne majalisar wakilan kasar ta kuduri aniyar jefa kuri'a game da yarjejeniyar ficewar kasar daga EU da gwamnatin Birtaniya da EU suka cimma. Amma a jajibirin ranar jefa kuri'ar, firaministar kasar Teresa May ta sanar da dage jefa kuri'ar ba zato ba tsammani, bisa dalilin cewar, akwai yiwuwar ba za'a amince da yarjejeniyar ba.
Teresa May ta jaddada cewa, 'yan majalisar wakilan kasar da dama sun goyi bayan wasu muhimman abubuwa da dama dake kunshe cikin wannan yarjejeniya, amma kuma sun nuna damuwa sosai kan batun iyakokin Birtaniya da Ireland bayan da ta fice daga EU.
Bisa yarjejeniyar da aka cimma a baya, Birtaniya za ta fice daga EU a ranar 29 ga watan Maris din bana.(Murtala Zhang)