in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin da Amurka sun kammala tattaunawarsu ta baya-bayan nan tare da samun kyawawan sakamako
2019-02-25 09:42:41 cri

Kasashen Sin da Amurka, sun samu ci gaba kan wasu batutuwa, biyo bayan tattaunawar baya-bayan nan da manyan jami'ansu suka yi, kan harkokin tattalin arziki da cinikayya da ta gudana a binin Washington.

Yayin tattaunawar da ta gudana daga ranar 21 zuwa jiya 24 ga wata, wadda kuma ita ce zagaye na 7 da suka yi, tun bayan fara irin tattaunawar a watan Fabrairun bara, jami'an kasar Sin da Amurka sun aiwatar da wasu muhimman matsaya da shugabannin kasashensu suka cimma, yayin ganawar da suka yi cikin watan Disamba a kasar Argentina, inda suka mayar da akalar tattaunawartasu kan daftarin yarjejeniya.

Wakilan kasar Sin sun ce an samu ci gaba a bangarorin da suka hada da musayar fasahohi da kare hakkin mallakar fasaha da sana'ar ba da hidima da harkokin gona da shingayen cinikayya da ba na haraji ba da farashin musayar kudade.

La'akari da ci gaban da aka samu, bangarorin biyu za su ci gaba da aiki domin shiga sabon mataki, bisa umarnin shugabannin kasashen biyu.

Tawagar kasar Sin na karkashin Liu He, mataimakin firaministan kasar wanda kuma shi ne manzon musammamn na shugaban kasar Sin Xi Jinping, yayin da tawagar Amurka ke karkashin wakilin kasar kan harkokin cinikayya Robert Lighthizer da sakataren ma'aikatar harkokin kudin kasar Steven Mnuchin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China