An bukaci Amurka ta rika kallon ci gaban kasar Sin da dangantakar dake tsakaninsu da kyakkywar manufa, tare da aiki da kasar Sin din bisa wannan turba.
Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma Ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ne ya bayyana hakan, lokacin da yake tattaunawa da tawagar Amurka, karkashin jagorancin mataimakin shugaban cibiyar bunkasa ciniki na kasar, Myron Brilliant a nan birnin Beijing.
Wang Yi ya ce mutunta juna da hadin kai domin moriyar juna ba su ne kadai zabi a garesu ba, har ma da buri guda game da al'ummomin duniya.
Ya kuma yi kira ga Amurkar, da ta rika daukar ci gaban kasar Sin a matsayin wata dama gareta, wadda za ta dace da magance wasu matsalolin dake tsakanin kasashen biyu. (Fa'iza Mustapha)