Yau Litinin, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang ya karyata kalaman da mataimakin shugaban kasar Amurka Mike Pence ya yi, inda ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin ba ta taba bukatar wani kamfani ko mutum don ya hada kai da gwamnati don yin leken asiri ba. Don haka kasar Sin tana fatan Amurka ta daina yin wa dokokin kasar gurguwar fahimta. Ko da yaushe gwamnatin Sin ta bukaci kamfanoninta da suka martaba dokokin kasashen da suke gudanar da ayyuka a ciki, kuma ba za ta canza wannan ra'ayi ba har abada.(Kande Gao)