Yayin ganawar da suka yi a jiya Juma'a a ofishin fadar shugaban kasar Amurka wato White House, Liu He ya isar da sakon shugaban kasar Sin Xi Jinping zuwa shugaba Trump, inda Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a kwanakin baya, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na kasashen biyu sun aiwatar da ra'ayoyin bai daya da shugabannin biyu suka cimma a ganawarsu a kasar Argentina, da yin shawarwari sau da dama tare da samun ci gaba. Ana fatan bangarorin biyu za su hada gwiwa da kokari tare bisa tushen girmama juna don cimma yarjejeniyar moriyar juna a tsakaninsu.
Liu He ya bayyana cewa, a wadannan kwanaki biyu, tawagogin kasashen biyu sun yi tattaunawa mai zurfi, da samun ci gaba a fannonin samun daidaiton ciniki da aikin noma da musayar da fasahohi da kiyaye ikon mallakar ilmi da bada hidimar hada-hadar kudi da sauransu. A mataki na gaba, bangarorin biyu za su kara yin kokari da tattaunawa da juna don aiwatar da ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka ba su cikin nasara.
A nasa bangare, shugaba Trump ya bayyana cewa, an samu babban ci gaba a tattaunawar ta wannan zagaye, amma akwai sauran ayyuka da dama da ake bukatar da gamawa, don hakan bangarorin biyu sun tsaida kudurin tsawaita tattaunawar har na tsawon kwanaki 2. Ya kara da cewa Amurka tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen sa kaimi ga samun karin sakamako a tattaunawar. Sannan ya ce ya yi imani cewa, bangarorin biyu za su cimma yarjejeniya mai babbar ma'ana da za ta kawo moriyar juna ga kasashen biyu. (Zainab)