Game da shawarwarin tattalin arziki da cinikayya da za a yi a 'yan kwanaki masu zuwa, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yau Talata a Beijing, cewar, ana fatan kasashen Sin da Amurka za su aiwatar da ra'ayoyin da shugabannin kasashen biyu suka cimma yayin ganawarsu a kasar Argentina, da yin kokari tare domin neman cimma wata yarjejeniyar moriyar juna da sassan biyu za su amince da ita. Hakan ya dace da muradun Sin da Amurka, kana shi ne burin da kasashen duniya ke da shi.(Kande Gao)