in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi: Ana fatan Amurka za ta yi kokari tare da Sin don aiwatar da ra'ayoyin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma
2019-02-17 16:44:21 cri

A ranar 16 ga wata bisa agogon wurin, Yang Jiechi ya jaddada cewa, game da rigingimun dake tsakanin Sin da Amurka ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, kasar Sin tana son warware shi ta hanyar hadin gwiwa. Amma irin hadin gwiwar zai shafi bin wasu ka'idoji. A 'yan kwanakin baya, tawagogin tattalin arziki da cinikayya na Sin da Amurka sun sha yin shawarwari a tsakaninsu, wadanda suka samu wasu ci gaba. Ana fatan bangarorin biyu za su kara kokari tare domin kara azama wajen cimma yarjejeniyar da za ta iya kawowa juna moriya.

Yang Jiechi, mamban hukumar siyasa ta kwamitin koli na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin kuma shugaban sakatariyar kwamitin kula da harkokin waje na kwamitin kolin jam'iyyar ya yi wannan furuci ne yayin da yake amsa tambayoyin da 'yan jarida suka yi masa bayan da ya ba da jawabi a yayin taron tsaro karo na 55 da aka yi a birnin Munich dake Jamus.

Ban da wannan kuma, Yang ya nuna cewa, gwamnatin kasar Sin na dora matukar muhimmanci kan sha'anin hakkin bil Adama, ganin yadda al'ummar Sin daga kalibu daban daban ke hadin gwiwarsu da nuna hazaka tare don samun kyautatuwar zaman rayuwarsu. Kasar Sin ta nuna matukar rashin yarda da Amurka ta zarge ta kan wannan batu ba tare da wani dalili ko hujja ba.

Haka zakila Yang ya nanata cewa, ko da yaushe gwamnatin kasar Sin ta bukaci kamfanoninta da suka bi dokokin kasa da kasa da ka'idojin kasashen da suke raya ayyukansu a ciki. Kamfanin Huawei ya bayar da babbar gudummawa ga ci gaban fasahohin sadarwa na wasu kasashe, ciki har da wasu dake nahiyar Turai, yayin da ya bi dokokin kasashen sosai. An yi imanin cewa, jama'ar kasashen Turai dake da dogon tarihi suna da basirar san abubuwan da za su dace da muradunsu. Sin tana son hadin kai tare da kasashen Turai wajen tinkarar wannan zamanin wajen raya masana'antu a zagaye na hudu, domin neman samun bunkasa ta bai daya.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China