in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya kai ziyarar aiki cibiyar shirya gasar wasan motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu
2019-02-02 16:51:45 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya kai ziyarar aiki cibiyar nune-nunen gasar wasan motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu, da cibiyar horo ta wasannin motsa jiki a lokacin hunturu dake yankin Shijingshan na birnin Beijing da yammacin jiya, domin duba yadda ake shirya gasar wasan motsa jiki da gasar nakasassu na Olympics na lokacin hunturu.

A cibiyar horo ta wasannin motsa jiki a yanayin sanyi, shugaba Xi ya yaba matuka da 'yan wasan, domin kokarin da suka yi na shiryawa gasar. Ya kuma ja hankalinsu game da yin atisaye bisa fasahohi yadda ya kamata, da kuma kulawa da lafiyar jikinsu.

Xi Jinping ya ce, za a daga darajar wasannin motsa jiki na yanayin sanyi a kasar Sin zuwa wani sabon matsayi, ta hanyar gudanar da gasar wasan motsa jiki ta Olympics a yanayin sanyi. Ya ce wannan kyakyyawar dama ce da kasar ta samu cikin darurruwan shekaru da suka gabata, kuma za a samu kwararrun 'yan wasan motsa jiki da dama a kasar. Ya kara da fatan cewa, za a raya wasannin motsa jiki a yanayin sanyi a kasar Sin ta hanyar gudanar da gasar motsa jiki ta Olympics a yanayin sanyi ta birnin Beijing. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China