in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da mai dakinsa sun gana da babban jami'in DPRK
2019-01-28 09:35:59 cri

Xi Jinping, babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kasar Sin, tare da uwar gidansa Peng Liyuan a ranar Lahadi sun gana da Ri Su Yong, wani babban jami'in gwamnatin Koriya ta Arewa DPRK, inda suka kalli wasannin al'adun gargajiya da 'yan wasan fasahar DPRK suka shirya.

Ri, mamba ne a hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar Workers' Party ta kasar, kuma mataimakin shugaban kwamitin tsakiya na jam'iyyar, kana daraktan hulda da kasa da kasa na jam'iyyar, ya kawo ziyarar sada zumunta da karfafa al'adu zuwa kasar Sin tare da tawagar 'yan wasan fasaha.

Wannan ziyara, tana da muhimmanci wajen musayar al'adu tun bayan aiwatar da yarjejeniyar da da bangarorin biyu suka cimma, da kuma muhimmin bikin cika shekaru 70 da kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da DPRK, kuma ziyarar za ta kasance wata babbar nasarar da za ta kara gina dangantaka tsakanin al'ummomin kasashen biyu, in ji shugaba Xi.(Ahmad fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China