in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya mika sakon fatan alheri na murnar bikin bazara ga 'yan jarida
2019-01-26 16:41:36 cri

A jiya Juma'a shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon fatan alheri na murnar bikin bazara ga dukkan 'yan jaridun kasar, inda ya nanata aniyar hade ci gaban fannonin yada bayanai.

Xi, wanda shi ne babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin aikin soja na kasar Sin, ya yi wannan tsokaci ne a lokacin taron hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar JKS, wanda ya shafi dukkan ayyukan kafafen yada labarai da ci gaban aikin jarida.

An gudana da taron ne a babban ginin jaridar People's Daily ta kasar Sin.

Xi ya jaddada cewa, ingantaccen ci gaban fannin jarida zai daga matsayin aikin yada labarai.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China