in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya mika gaisuwar sabuwar shekara ga wadanda ba 'yan JKS ba
2019-01-29 14:35:57 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci wani taro jiya Litinin a nan birnin Beijing, inda ya mika gaisuwar murnar shiga sabuwar shekara ga shugabannin jam'iyyun da ba na kwaminis ba da kungiyar masana'antu da ciniki ta kasar (ACFIC) da kuma mutanen da ba su da jam'iyya.

Xi Jinping wanda shi ne sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana fatan za su ba da sabuwar gudunmuwa ga raya al'umma mai kyakkywar makoma a dukkan fannoni.

Shugaba Xi ya ce, cikin shekarar da ta gabta, kasar Sin za ta ci gaba da samun bunkasar tattalin arziki cikin yanayi mai kyau, yana mai cewa, an inganta sauye-sauyen da aka gudanar cikin tsarin jam'iyyar, da ma kasar, tare da sauran gyare gyare, kuma matakin bude kofa na kasar Sin na kara samun ingantuwa.

Ya kuma yi kira ga jam'iyyun da ba na kwaminis ba da kungiyar ACFIC da sauran mutanen da ba su da jam'iyya, da su hada kan jama'a wajen inganta gyare gyare da samun ci gaba, yana mai kira da su rika bibiyar dabaru da matakan kwamitin tsakiya na JKS tare da bayyana kwarewa da hikimarsu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China