in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi ya aike da sakon ta'aziyya ga Brazil sakamakon ballewar dam
2019-01-26 20:55:13 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping a yau Asabar ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Brazil Jair Bolsonaro, sakamakon ballewar madatsar ruwa wanda ya haifar da gagarumar hasara a kasar kwana guda ke nan da faruwar lamarin.

A cikin sakon da ya aike da shi, Xi ya ce, ya yi matukar kaduwa da samun labarin ballewar dam din a jihar Minas Gerais, wanda kuma ya haddasa hasarar dunbun dukiya.

A madadin gwamnatin kasar Sin da al'ummar kasar, Xi ya mika sakon ta'aziyya tare da jajantawa iyalan wadanda ibtila'in ya rutsa da su da wadanda suka bace, sannan yana taya al'ummar kasar Brazil jimami game da afkuwar lamarin.

Sannan ya yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.

Bisa labarin da hukumar 'yan kwana-kwana ta kasar Brazil ta bayar da sanyin safiyar ranar 26 ga wata, an ce, an samu hadarin ballewar dam dake jihar Minas Gerias a ranar 25 ga wata, wanda ya haddasa mutuwar mutane 9, kana mutane kimanin 300 sun bace.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China