Cikin sakonsa, shugaba Xi ya jaddada cewa, kasar Sin tana kin jinin duk wani irin aiki na ta'addanci, kuma tana Allah wadai da hare-haren da aka kai wa fararen hula, wadanda ba su san hawa ba, ba su san sauka ba. Ya ce kasar Sin tana da burin aiki tare da Philippines, gami da sauran kasashe daban daban, don yaki da ta'addanci, da tabbatar da kwanciyar hankali a duniyarmu. (Bello Wang)