Ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan yiwa kungiyar WTO gyare-gyare, domin kara karfin kungiyar wajen gudanar da ayyukanta, kana, Sin tana ganin cewa, ya kamata a yiwa kungiyar kwaskwarima bisa ka'idoji guda hudu.
Da farko, ya kamata a kare muhimman ka'idojin kungiyar, mu tsaya tsayin daka kan inganta harkokin 'yancin ciniki. Na biyu shi ne, Ya kamata a martaba manufar tuntubar juna da sasantawa, kasar Sin tana adawa da yunkurin kafa wasu kungiyoyin da saura ba za su shiga ciki ba. Sa'an nan kuma, ya kamata a taimakawa kasashe masu tasowa yadda ya kamata, kasar Sin tana fatan kasar Faransa za ta mutunta kasar Sin a matsayinta na kasa mai tasowa. A karshe dai, ya kamata a warware batun zabar mambobin hukumar daukaka kara da farko.
Bugu da kari, Mr. Wang ya ce, cikin shawarwarin da aka yi a wannan rana, kasar Faransa ta jaddada adawarta kan ra'ayin kashin kai, ta kuma nuna goyon baya ga tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa, lamarin da ya janyo hankalin kasar Sin kwarai da gaske. Kasar Sin tana fatan karfafa hadin gwiwa da mu'amala tsakaninta da kasar Faransa da ma kungiyar tarayyar kasashen Turai bisa ka'idojin nuna adalci da fahimtar juna, domin kyautata tsarin ciniki tsakanin kasa da kasa, ta yadda zai dace da halin da muke ciki da kuma taimakawa kungiyar WTO wajen karfafa ayyukan raya tattalin arzikin duniya. (Maryam)