in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta rage hasashen karuwar cinikayyar duniya a bana da shekara mai zuwa
2018-09-27 21:04:16 cri
Yau Alhamis, hukumar WTO ta sanar da cewa, ta rage hasashenta kan karuwar cinikayyar duniya a shekarar bana da ma mai zuwa, sakamakon tsanantar takaddamar cinikayya dake tsakanin wasu manyan kasashe a fannin tattalin arziki, da tsaurara manufofi na kudi da kasashe masu ci gaba suke yi.

Hukumar ta sanar da cewa, ta rage hasashen karuwar cinikayyar kayayyakin na shekarar 2018 daga 4.4% da ta yi a watan Aflilu zuwa 3.9%, kana ta rage hasashen karuwar cinikayyar shekara mai zuwa daga 4.0% zuwa 3.7%. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China