in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu mambobin WTO na neman bincika matakan buga karin harajn kwastam da Amurka ta dauka
2018-10-31 11:44:32 cri
A ranar Litinin da ta gabata, a yayin wani taron hukumar daidaita matsalolin rigingimu ta WTO, mambobin kungiyar 7, wato kasashen Sin da kungiyar EU da Canada da Mexico da Norway da Rasha da Turkiyya sun nanata cewa, matakan buga karin harajin kwastam kan kayayyakin korafu da na sanholo da kasar Amurka ta sanar a watan Maris ba tare da yin la'akari da "tsaron kasa" ba, a hakika mataki ne na kariyar cinikayya, saboda haka, sun nemi a kafa wani rukunin masana domin yin bincike ko wannan matakin da kasar Amurka ta dauka ya saba da ka'idojin kungiyar WTO ko kuma a'a.

A ranar 8 ga watan Maris na bana, shugaba Donald Trump na Amurka ya shelanta cewa, saboda kayayyakin korafu da na sanholo da ake shigo da su daga waje sun kawo illa ga tsaron kasar Amurka, kasar Amurka za ta buga karin harajin kwastam da kashi 25 cikin dari da kuma kashi 10 cikin dari kan wadannan kayayyaki. Wannan matakin da gwamnatin Trump ta dauka ya fara aiki daga ranar 23 ga watan Maris ga kayayyakin korafu da na sanholo na galibin mambobin kungiyar WTO, sannan ya fara aiki ga irin wadannan kayayyakin da aka shigar kasar Amurka daga kasashen EU da Canada da Mexico a ranar 1 ga watan Yuni. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China