Bugu da kari, dole ne a tsaya kan matsayin shimfida dimokuradiyya, da kuma daukar matakan magance nuna bambanci ga kowane mamba. Sannan Mr. Zhang ya bayyana cewa, nauyin da dole ne a sauke shi yanzu cikin gaggawa su ne, komawa ga tsarin daidaita hargitsi na WTO kamar yadda ya kamata. Sannan ya kamata a yi kokarin samun ci gaba, wajen yin shawarwari kan yarjejeniyar tallafawa sana'ar kamun kifi, da batutuwan da suke shafar masan'anatu, da kamfanoni matsakaita da kanana, da kuma yin cinikayya ta yanar gizo, da saukaka sharudan zuba jari da dai makamantansu.
Bugu da kari, Zhang Xiangchen ya ce, kasar Sin da kungiyar kawancen kasashen Turai wato EU,sun riga sun kafa wani rukuni mai kunshe da wasu manyan jami'ansu kan batun gyara fuskar kungiyar WTO, sannan sun riga sun kammala shirin yin kwaskwarima ga hukumar kai kara ta WTO. A waje daya kuma, za su soma tattaunawa kan sauran batutuwan gyaran fuskar WTO. Bugu da kari, kasar Sin ita kanta, za ta gabatar da shirinta na gyaran fuskar WTO nan ba da dadewa ba. (Sanusi Chen)