in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WTO ta yarda da kafa kungiyar kwararru don binciken matakin karbar harajin kwastan da Amurka ta dauka kan ingantaccen bakin karfe da karfen goran ruwa
2018-11-22 16:32:01 cri
Jiya hukumar warware takaddama ta kungiyar WTO ta kira taro, inda aka amince da bukatun mambobin kungiyar guda bakwai, ciki har da Sin, tarayyar Turai, Canada, Mexico, Norway, Rasha da Turkiyya, na kafa kungiyar kwararru don binciken matakin da Amurka ta sanar a watan Maris, game da sanya harajin kwastan kan ingantaccen bakin karfe da karfen goran ruwa, wadda za ta duba ko matakin ya taka dokokin kungiyar ko a'a.

A ranar 8 ga watan Maris, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa, kayayyakin ingantaccen bakin karfe, da karfen goran ruwa na kawo illa ga tsaron kasar sa, don haka kasar Amurka za ta karbi haraji na kashi 25% da kashi 10% kan su. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China