in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin na goyon bayan WTO wajen yin kwaskwarima
2018-12-14 13:51:21 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya bayyana a jiya Alhamis cewa, kasar Sin zata yi hadin gwiwa da mambobin kungiyar kasuwanci ta duniya wato WTO wajen kiyaye ka'idojin kungiyar da kuma kara karfinta wajen gudanar da ayyukanta. A sa'i daya kuma, kasar Sin zata kara inganta matakanta na bude kofa ga waje, domin yin hadin gwiwa da kasa da kasa wajen gina tsarin ciniki mai bude kofa ga waje, ta yadda za'a cimma moriyar juna.

Shekarar bana, shekara ce ta cika shekaru 17 da kasar Sin ta shiga kungiyar WTO, kwanan baya, kakakin kungiyar WTO ya bayyana cewa, kasar Sin ita ce muhimmiyar mamba ta kungiyar WTO, wadda ta bada gudummawa matuka wajen kiyaye tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang ya ce, cikin shekaru 17 da suka gabata, kasar Sin ta goyi bayan kungiyar WTO bisa dukkan fannoni, ta kuma bada gudummawa cikin harkokin inganta 'yancin ciniki, tana kuma daga cikin kasashen da suka fara da kulla yarjejeniyar samar da sauki ga cinikayya, ta kuma goyi bayan kasashe masu tasowa dasu shiga cikin cinikin kasa da kasa.

A sa'i daya kuma, Lu Kang ya jaddada cewa, muna cikin muhimmin lokaci ta fuskar tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban, saboda a halin yanzu, kariyar ciniki na haifar da babban kalubale ga wannan tsari. Dangane da haka, kasar Sin zata tsaya tsayin daka kan karfafa tsarin cinikin dake tsakanin bangarori daban daban, kuma zata goyi bayan kungiyar WTO wajen yin gyare-gyare yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China