in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin kudi ta Amurka ta sanar da kakabawa kamfanoni da kungiyoyi masu alaka da Iran guda 4 takunkumi
2019-01-25 10:56:16 cri
Jiya Alhamis, ma'aikatar harkokin kudi ta kasar Amurka ta sanar da kakabawa kamfanoni da kungiyoyi masu alaka da kasar Iran guda 4 takunkumi.

Wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar na cewa, wadannan kamfanoni da kungiyoyi sun hada da, kungiyoyin tsageru guda biyu dake gudanar da harkokinsu a kasar Syria, wadanda suke samun goyon baya daga kasar Iran, da wani kamfanin jiragen saman fasinja reshen kamfanin jiragen sama na Mahan Air na kasar Iran, da kuma wani kamfanin Armenia dake samar da hidima ga kamfanin Mahan Air na Iran.

Bisa dokar kasar Amurka, za a rike kudade da kadarori na wadannan kamfanoni da kungiyoyi dake kasar Amurka, haka kuma, an hana Amurkawa yin duk wata huldar ciniki da wandanan kamfanoni da kungiyoyi.

A watan Mayu na shekarar 2018, gwamnatin kasar Amurka ta sanar da janyewa daga yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran da aka kulla a watan Yuli na shekarar 2015. Sa'an nan, ta sake kakabawa kasar takunkumin da ta taba dakatar da su bayan aka kulla yarjejeniyar. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China