Game da batun sake kakabawa Iran takunkumi da Amurka ta yi, Seyyed Ali Khamenei ya ce, mutanen Amurka na ganin cewa takunkumin da aka sanya ya kasance wanda ba'a taba ganin irinsa ba a tarihi, amma ina tabbatar da cewa su ma za su ji kunya wadda ba'a taba ganin irinta ba a tarihi.
Khamenei ya ce, takunkumin da Amurka ta sanyawa Iran yana matsawa kasar gami da al'ummarta lamba, yana bukatar jami'an gwamnatin Iran da su maida hankali kan bangaren zaman rayuwar al'umma, da bada fifiko kan tallafawa mutane masu fama da talauci, tare kuma da inganta kwarewar matasan kasar.
Khamenei ya sake jaddada cewa, ya kamata a kwantar da hankali yayin da ake fuskantar ayyukan da Amurka da Turai suke yi, inda ya ce, barazana da alkawari ko kuma sanya hannun da suka yi duk ba za'a iya yarda da su ba.(Murtala Zhang)