"Iran tana daya daga cikin manyan kasashen duniya dake sahun gaba wajen kera makamai masu linzami, da jiragen sama masu bincike, da manyan tankokin yaki da sauran motocin dake daukar makamai," in ji Hatami ya fadawa kamfanin dillancin labaran kasar IRNA.
"Iran ta samu nasarar kaiwa matsayin da take son kaiwa da kuma kokarin da take yi a bangaren samar da makamai don kare kanta da al'ummar Iraniyawa, ma'aikatar tsaron Iran ta kasance mai cin gashin kanta ta fuskar tsaro duk da irin matsin lambar da take fuskanta daga kasashen duniya masu ji da kansu a cikin shekaru 40 da suka gabata," an jiyo Hatami yana wadannan kalamai. (Ahmad Fagam)