in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta soki takunkuman da Amurka ta saka mata a matsayin ta'addanci kan tattalin arziki
2018-12-09 16:41:00 cri

Shugaban Iran Hassan Rouhani, ya soki matakan Amurka na kakabawa kasarsa takunkumi, yana mai bayyana yunkurin a matsayin ta'addanci kan tattalin arziki.

Yayin taron kasa da kasa kan kalubalen ta'addanci, Shugaba Rouhani ya yi bayanin cewa, ta'addanci kan tattalin arziki na nufin haifar da fargaba game da tattalin arzikin wata kasa tare da hana sauran kasashe zuba jari da aiwatar da cinikayya da ita.

Ya ce janyewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran tare da mayar da takunkumai kan kasar da matsawa abokan cinikayyarta lamba, babban misali ne na ta'addanci kan tattalin arziki.

An kaddamar da taron ne jiya Asabar a Tehran babban birnin Iran, inda wakilai daga kasashen Afghanistan da Sin da Pakistan da Rasha da Turkiyya suka halarta.

Shugaban na Iran ya jaddada cewa, sun hadu ne da nufin sanar da cewa, Amurka ta yi babban kuskure idan ta dauka za ta iya raba kansu. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China