Bahram Qassemi ya bayyana cewa, girke sojoji a yankin Gabas ta Tsakiya wani mataki ne da gwamnatin Amurka ta dauka bisa kuskure da rashin tunani, wanda kuma ya haddasa rikici a yankin. Bahram Qassemi ya ce, idan aka dubi yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, za'a iya gano cewa, jibge sojojin Amurka a wajen ya tsananta halin da ake ciki gami da haifar da tashe-tashen hankali, kuma sam bai yi tasiri mai kyau ba.
Rahotannin da aka ruwaito sun ce, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa za'a janye sojojin kasarsa daga kasar Siriya nan bada jimawa ba, al'amarin da ya haddasa neman yin murabus din ministan tsaron kasar Amurkar, James Mattis. (Murtala Zhang)