in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mambobin EU dake cikin kwamitin sulhun MDD sun sha alwashin shiga yarjejeniyar nukiliyar Iran
2018-12-13 10:21:48 cri
Kasashe mambobin kungiyar tarayyar Turai EU dake cikin kwamitin sulhun MDD a jiya Laraba sun bayyana aniyarsu na goyon bayan yarjejeniyar nukiliyar kasar Iran.

"Mu, a matsayinmu na mambobin EU a kwamitin sulhun MDD, muna so mu bayyana aniyarmu da cikakken goyon bayanmu na tabbatar da cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar JCPOA da kudurin doka mai lamba 2231," kungiyar ce ta sanar da hakan, ta yi amfani da taken da aka baiwa yarjejeniyar da kuma kudurin da kwamitin sulhun ya amince da shi.

"An tabbatar da cewa Iran tana cigaba da aiwatar da yarjejeniyar data shafi batun nukiliyar kasar. Cikakkiyar yarjejeniyar ta JCPOA ta yi babban tasiri wajen maido da shirin yarjejeniyar nukiliyar ta Iran, kuma ta tabbatar da cewa Iran ba ta koma shirinta na kera makaman nukiliya ba. Wannan muhimmin batu ne ga al'amurran tsaron Turai."

Matukar dai Iran ta ci gaba da ba da himma wajen cikakkiyar aiwatar da yarjejejniyar, EU za ta ci gaba da nuna goyon bayanta ga kokarin aiwatar da yarjejeniyar, in ji wadannan mambobin kungiyar EU. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China