in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Iran ta musunta labarin da aka bayar cewa wai za ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliyar ta
2019-01-14 10:51:58 cri
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na Tasnim na kasar Iran ya bayar a ranar 13 ga wata, an ce, ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ta musunta labarin da ake yadawa, cewa wai Iran za ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliyar ta.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahram Qasemi ya bayyana cewa, a kwanakin nan, akwai labarin da ake yadawa, cewa wai Iran za ta janye daga yarjejeniyar batun nukiliyar ta, labarin da ya ce sam ba shi da tushe.

Wasu kungiyoyin musamman na kasar Iran sun fitar da irin wannan labari don kimsa tsoro a tsakanin al'ummar kasar, da samun moriyar kashin kai.

Jami'in ya ce, hukumomin koli na kasar Iran sun tsaida dukkan kuduri game da yarjejeniyar batun nukiliyar kasar.

A wannan rana, shugaban hukumar makamashin nukiliya ta kasar Iran Ali Akabar Salehi, ya bayyana wa wakili na gidan telebijin na kasar Iran cewa, kasar Iran ta samu babbar nasara a fannin fasahar makamashin nukiliya, kuma ta riga ta shirya samar da sabon makamashin nukiliya. Amma bai bayyana wane irin makamashin nukiliya za a samar ba. Ya ce, a halin yanzu Iran tana da karfin samar da na'urar sarrafa nukiliya da kanta. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China