Xia Huang ya shafe shekaru 30 yana aikin diflomasiyya, ya kuma yi aiki a kasashen Afirka da dama. Daga shekarar 2015 zuwa shekarar 2018, ya zama jakadan kasar Sin a kasar Congo-Brazzaville.
Yankin manyan tafkuna Afirka dai yana tsakiyar gabashin nahiyar Afirka, wato yankunan dake kewaye da kuma kusa da tabkin Victoria, tabkin Tanganyika da kuma tabkin Kivu.
A halin yanzu, yankin ya kasance wurin dake fama da matsalolin rikice-rikice, karancin abinci, da kuma 'yan gudun hijira, sakamakon hare-haren da suka addabi yankin. Lamarin da ya sa ake kira yankin "gangar albarushi na nahiyar Afrika". (Maryam)