in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Kamaru zasu inganta hadin gwiwa
2019-01-19 20:24:14 cri
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, Yang Jiechi, da shugaban kasar Kamaru Paul Biya, sun amince a ranar Juma'a zasu kara karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Paul Biya ya kai ziyarar aiki kasar Sin a shekarar data gabata kuma ya halarci taron kolin Beijing na dandalin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afrika wato (FOCAC), inda aka cimma daidaito da Xi, in ji Yang, ya kara da cewa, dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta kai wani babban matsayi a tarihi tare da samar da wasu muhimman damammakin raya cigaba.

Yang ya ce, makasudin ziyarar shi ne domin kara karfafa musayar bayanai da bangaren Kamaru da kuma ingiza aiwatar da muhimman yarjejeniyoyi da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu bisa ga sakamakon taron kolin, da nufin daga matsayin abokantakar bangarori zuwa matsayin koli.

A nasa bangaren, Biya yace Kamaru tana dora muhimmanci kan dangantakar dake tsakaninta da kasar Sin, da nuna godiya bisa taimakon da kasar Sin ke baiwa kasarsa, kana yana fatan kasar Sin zata kara samun nasarori a yunkurinta na neman bunkasuwa.

Biya ya ce, Kamaru tana maraba da shawarar ziri daya da hanya daya, kuma tana goyon bayan hadin gwiwar bangarorin kasashen karkashin dandalin FOCAC.

Kamaru a shirye take tayi aiki tare da kasar Sin wajen aiwatar da kudurorin da aka cimma sakamakon taron kolin Beijing, da kuma daga matsayin dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa sabon matsayi, inji Biya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China