in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari a tsakanin ministocin harkokin wajen Zambia da Afirka ta kudu
2019-01-08 09:59:05 cri
Jiya Litinin aka yi shawarwari a tsakanin kasashen Zambia da Afirka ta kudu da nufin karfafa dangantakar dake tsakaninsu.

Wata sanarwa da ofishin jakadancin Zambia dake Afirka ta kudu ya bayar, ta ce ministan harkokin wajen kasar Zambia Joseph Malanji da takwaransa na kasar Afirka ta kudu Lindiwe Sisulu sun yi shawarwari a Pretoria.

Sanarwar ta ce, daga cikin abubuwan da aka tattauna har da shirye-shiryen da ake kan taron hukumar na kasashen biyu da zai gudana a cikin watanni uku na faron shekarar da muke ciki.

A watan Agustan bara, kasashen biyu sun sa hannu kan hadaddiyar hukumar kasashen biyu da nufin inganta cinikayya a tsakaninsu.

Hukumar dake karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu za ta taimaka wajen inganta cinikayya tsakanin kasashen biyu, da daidaita cinikayya, kayayyakin shigi da fici, batun bakin haure da kuma yanke hukunci kan dokoki da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China