in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a gudanar da bikin baje kolin tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Afirka
2019-01-11 10:50:55 cri
Kasar Sin zata karbi bakuncin bikin baje kolin tattalin arziki da ciniki tsakanin Sin da Afirka irinsa na farko a Changsha, babban birnin lardin Hunan tsakanin 18 zuwa 20 ga watan Yuni.

Bikin da ake saran filinsa zai kai sikwaya mita 50,000, zai baje kolin damammakin tattalin arziki da ciniki na kasashen Sin da Afrika, masu shirya bikin ne suka bayyana hakan a jiya Alhamis.

Za kuma a gudanar da bikin sanya hannu kan manyan yarjejeniyoyi ciniki da tattalin arziki a lokacin bikin baje kolin, da wasu jerin tarurrukan zuba jari da za'a yi a lokacin bikin, kana da shawarwarin cinikayya wadanda za'a gudanar.

Baje kolin, za'a gudanar da shi ne karkashin lemar dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika, zai samar da sabbin matakan raya hadin gwiwar ciniki da tattalin arziki tsakanin Sin da kasashen Afrika, in ji Li Chenggang, mai taimakawa ministan harkokin kasuwanci na kasar Sin.

Karfin jarin ciniki tsakanin yankin Hunan da kasashen Afrika ya kai na dala biliyan 2.8 a shekarar 2018, in ji mataimakin gwamnan Hunan, He Baoxiang. Jarin da kamfanonin Hunan suka zuba a kasashen Afrika ya kai kusan dala biliyan 1.

Za'a dinga gudanar da baje koli ne a lardin sau daya a duk bayan shekaru biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China