Bayan wadannan 'yan jaridu sun ziyarci dakin nune-nunen harkokin yaki da ta'addanci na jihar Xinjiang, dukkansu sun bayyana cewa, ta'addanci shi ne abokin gabar dukkanin bil Adama, ya kamata kasashen duniya su yi hadin gwiwa domin fuskantar wannan matsala. Kuma kasar Sin ta dauki matakai yadda ya kamata, wadanda za su tabbatar da zaman lafiya a jihar Xinjiang.
Haka kuma, shugaban kungiyar 'yan jaridu ta Izmir ta kasar Turkiya Misket Dikmen ya bayyana cewa, cikin dogon lokacin da suka gabata, kasar Turkiya tana fama da matsalar ta'addanci, shi ya sa, kasarsa ta fahimci damuwar kasar Sin sosai ta fuskar wannan aiki. Ya ce, nune-nunen da suka kalla a wannan rana, sun nuna tashe-tashen hankula da rasuwar mutane da 'yan ta'adda suka kawo mana. A ganinsa, nunawa al'ummomin kasa da kasa game da mugun laifukan da 'yan ta'adda suka aikata ya kasance wani mataki mai karfi, ta yadda kowa zai gani da idonsa, kuma za a fahimci wannan batu yadda ya kamata. (Maryam)