'Yan jaridun sun nuna amincewa da yabo, ga ayyukan kiyaye al'adun gargajiya da aka gada daga kaka da kakanni da ake gudanarwa a wurin.
Tawagar wadda ta soma ziyara a kasar Sin daga ranar 7 ga wata, na kunshe da 'yan jaridu guda 12, wadanda suka zo daga wasu kasashe 6, ciki har da Masar, da Turkiyya, da Pakistan, da Afghanistan, da Sri Lanka da kuma Bangladesh. (Murtala Zhang)