in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta kalubalanci wasu kasashe su nuna gaskiya wajen duba matakan kiyaye zaman karko da Sin ke dauka a jihar Xinjiang
2018-12-25 10:34:57 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Hua Chunying a jiya Litinin ta kalubalanci jami'ai da kafofin watsa labaru na wasu kasashen yamma da su yi watsi da ra'ayi mai son zuciya, don nuna adalci da gaskiya wajen duba matakan kiyaye zaman karko da kasar Sin ta dauka a jihar Xinjiang mai ikon aiwatar da harkokin kanta ta kabilar Uygur.

Jaridar Wall Street ta bayar da rahoto a kwanan baya cewa, a cikin shekara guda da ta wuce, kasar Sin ta kara daukar matakan sa ido, da tsarewa da kuma yada manufa a jihar Xinjiang ta kasar, kana kuma ta dauki irin matakan ma a sauran yankunan musulmai na kasar. Game da wannan, madam Hua ta karyata a yayin taron manema labaru cewa, 'yan siyasa da kafofin watsa labarun wasu kasashen yamma sun yi babban kuskure kan batun jihar Xinjiang. Wato sun mai da kokarin da Sin ke yi na yaki da ta'addanci da kiyaye zaman karko da kuma kawar da tsattsauran ra'ayi a matsayin matakin da kasar ta dauka na musamman kan 'yan kabilar Uygur ko kuma musulmai.

Hua ta jaddada cewa, da farko, ko da yaushe gwamnatin kasar Sin na daukar matsayin adawa da yin alaka a tsakanin ta'addanci da kowane kabilu da addinai. Na biyu, kabilar Uygur tana daya daga cikin babban iyalin kasar Sin dake kunshe da kabilu 56. Na uku, game da wadancan da aka yi musu tasiri sakamakon ta'addanci da tattsauran ra'ayi, jihar Xinjiang ta dauki matakai masu dacewa, ciki har da ba su horo a fannin fasahohi na sana'o'i daban daban, don taimaka musu wajen koyon harshe, dokoki, da kuma fasaha, da kawar da sarrafawa da tasirin da aka kawo musu sakamakon ta'addanci da tsattsauran ra'ayin addini, don su sake komawa hanyar zaman rayuwarsu yadda ya kamata. Na hudu, ajiye wasu na'u'orin sa ido mataki ne da kasashe daban daban ke dauka don kiyaye tsaro da zaman karko. Me ya sa kasashen yamma sun yi haka ne domin kiyaye hakkin bil Adama, amma kasar Sin ta yi haka an ce wai ta keta hakkin bil Adama? Gaskiya kasashen yamma sun dauki ma'auni biyu kan wannan batu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China