in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban jihar Xinjiang ya amsa tambayoyin manema labarai game da ayyukan yaki da ta'addanci da tabbatar da zaman lafiya a jihar
2018-10-16 13:44:26 cri
A kwanakin baya ne, shugaban jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta ta kasar Sin, Xuekerat Zakir, ya amsa tambayoyin da manema labaran kamfanin dillancin labarai na Xinhua suka yi masa, dangane da yadda jiharsa ke kokarin murkushe ayyukan ta'addanci, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, da kuma samar da horon fasahohin gudanar da sana'o'i daban-daban.

Xuekerat Zakir ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharsa wato Xinjiang, kuma ba'a samu barkewar wani aikin ta'addanci cikin watanni 21 ba, kana, an samu raguwar adadin munanan laifuffukan da aka aikata a jihar, wadanda suka hada da yin barazana ga yanayin tsaro da zaman lafiyar al'umma. Ana kuma kara samun kyautatuwar yanayin tsaro a jihar Xinjiang, da kokarin yaki da mutane masu kaifin kishin addini, al'amarin da ya sa jama'ar kabilu daban-daban ke kara jin dadin zaman rayuwarsu a jihar cikin kwanciyar hankali, da aza tubali mai inganci wajen shimfida dauwamammen zaman lafiya.

Xuekerat Zakir ya kara da cewa, domin yaki da ayyukan ta'addanci gami da ra'ayin kaifin kishin addini, ya zama dole a horas da mutane don su nakalci fasahohin yin sana'a. Makasudin yin haka shi ne, murkushe ayyukan ta'addanci da mutanen dake da tsattsauran ra'ayin addini daga tushe, yana mai cewa rigakafi ya fi magani.

Har ila yau, Xuekerat Zakir ya ce, ta hanyar halartar irin wannan horo, akasarin mutane sun kara fahimtar gaskiya gami da babbar barazanar da ayyukan ta'addanci da ra'ayin kaifin kishin addini suka haifar, har ma sun kara kyautata fahimtarsu game da ra'ayin kishin kasa, da abubuwan da ya kamata su yi da abubuwan da bai kamata su yi ba, wato ra'ayin bin doka da oda. Bugu da kari, ta hanyar halartar irin wannan horo, jama'a sun kara samun kwarewa da basira wajen tantance gaskiya da yaki da ra'ayin kaifin kishin addini, da nuna himma da kwazo wajen neman samun wadata da yaki da fatara, abun da ya sa suka kara nuna kyakkyawan fata da imaninsu game da rayuwarsu na nan gaba.(Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China