Cikin takardar, an bayyana cewa, tun bayan kafuwar jamhuriyyar jama'ar kasar Sin, ya zuwa yanzu, gwamnatin kasar tana mai da hankali kwarai wajen kiyaye da kuma raya al'adun kabilu daban daban dake jihar Xinjiang, ta kuma yi kokarin ganin al'ummomin kabilu daban daban na jihar sun koyi harsunan juna, domin karfafa mu'amalar dake tsakanin al'ummominsu da mutunta 'yancin su na bin ko wane irin addini da kuma inganta harkokin al'adu a jihar, ta yadda al'ummomin kasar za su kara amincewa da kaunar al'adun juna. (Maryam)