Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, ya ce wasu kafofi dake adawa da kasar Sin suna kokarin shafa mata kashin kaji ne don biyan bukatunsu na siyasa.
A ranar 10 da kuma 13 ga watan Agusta ne yayin zamansa na 96 kwamitin yaki da nuna wariyar launin fata na MDD ya yi bitar yanayin da ake ciki a kasar ta Sin .
Lu ya ce tawagar kasar Sin yayin zaman ta yi bayani dalla-dalla game da ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kare 'yancin kananan kabilu kuma kwamitin ya tabbatar da kokari da ma nasarorin da gwamnatin kasar Sin ta cimma a wannan fanni.
A halin yanzu, komai ya dai-daita a yankin na Xinjiang, yanayin ci gaban tattalin arzikin yankin abin a yaba ne, kana dukkan kabilu na zama da juna cikin lumana. (Ibrahim)