in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tawagar jirage masu saukar ungulu ta Sin ta kammala aikin kiyaye zaman lafiya na farko na shekarar 2019
2019-01-06 17:05:18 cri
A ranar 3 ga wata, tawagar jirage masu saukar ungulu rukuni na biyu da kasar Sin ta tura birnin Darfur na kasar Sudan, ta kammala aikin kiyaye zaman lafiya na farko na shekarar 2019.

Yanayi na wancan rana ba shi da kyau, lumshi ya rufe sama da kuma iska mai karfi, kana akwai kurar kasa a cikin iska. Wani jirgin sama mai saukar ungulu samfurin MI-171 ya tashi daga filin jiragen sama na El Fasher dake jihar Darfur ta Arewa da misalin karfe 10 da rabi na safe, domin jigilar mutane 16 na tawagar hadin gwiwa ta musamman da kungiyar AU da MDD suka tura birnin Darfur wato UNAMID, da kayayyaki mai nauyin kilo dari 4 zuwa wurare biyu dake da nisan kilomita sama da dari daya. Sannan jirgin saman ya dawo filin jiragen sama na El Fasher da karfe 1 da minti 45 da yamma.

Bisa labarin da aka samu, an ce, bayan Sin ta tura tawagar jirage masu saukar ungulu rukuni na biyu zuwa birnin Darfur na kasar Sudan, ya zuwa yanzu, watanni 4 ke nan da suka gabata. Kuma cikin wadannan watanni 4, tawagar ta kammala manyan ayyuka masu wahala da dama da suka hada da gudanar da aikin ceto a yankin, hana shawagin jiragen sama dake tsaunin Marra, jigilar wadanda suka jikkata zuwa asibitoci da kuma jigilar harsasai da dai sauransu. Gaba daya tsawon lokacin tafiyar jiragen saman tawagar ya kai awo'i 320, inda suka yi jigilar mutane sama da 1100, da kuma kayayyaki kusan ton 120. Lamarin da ya sa UNAMID ta kira tawagar da suna "tawagar da ba za mu iya raba ta da sama ba." (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China