in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na himmatuwa wajen halartar ayyukan shimfida zaman lafiya na MDD
2018-05-30 15:24:12 cri

Ranar 29 ga watan Mayun bana, rana ce ta cika shekaru saba'in da MDD ta kaddamar da ayyukan wanzar da zaman lafiya a duk fadin duniya. Tun wannan karnin da muke ciki, kasar Sin ta himmatu wajen shiga ayyukan wanzar da zaman lafiya na MDD, don daukar nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa a duniya.

Ma'anar kalmar "zaman lafiya" a bangaren dama na haruffan Sinanci na nufin wani nau'in sharewa, yayin da harafin hagunsa ke nufin busawa. Don haka wannan kalma na nufin busa sharewa da farko, daga baya kuma ta fadada, duk da cewa akwai bambancin ra'ayoyi, amma babbar manufarsu ba ta canja ba.

Duk da cewa, akwai kamanceceniya da bambance-bambancen ra'ayi, yana daya daga cikin muhimman abubuwa na al'adun kasar Sin. Yayin da sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin ke gudanar da ayyukansu karkashin laimar MDD, suna kokarin yayata irin wannan ra'ayi a duk fadin duniya baki daya.

Duk da cewa launin fata da harshe da kuma al'adunmu ba daya ba ne, amma irin wadannan bambance-bambance sun zama wani muhimman sharadi ga neman samun kamanceceniya, abun da ya zama burin da muke kokarin cimmawa tare.

 

'Yan sandan kwantar da tarzomar kasar Sin suna sintiri a titunan kasar Liberiya.

Sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin suna halartar atisayen kwashe mutanen da suka jikkata a kasar lebanon.

Yara a Jamhuriyar Demokuradiyyar Kango suna mikawa sojojin kasar Sin furanni.

Reshen likitoci na sojojin kiyaye zaman lafiya na kasar Sin suna nunawa wasu mazauna a kasar Laberiya yadda za'a yi amfani da magani.

Wani likita na sojojin kiyaye zaman lafiyar kasar Sin yana duba marasa lafiya a birnin Gao na kasar Mali.

'Yan sandan kwantar da tarzoma na kasar Sin suna samar da jinya ga wasu yara a kasar Laberiya.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China