A cewar ma'aikatar kula da tsaron al'umma ta kasar Sin, ayarin 'yan sandan mai mambobi 12 shi ne kashi na 17 da za a tura Sudan ta Kudu, inda za su kama hanya a ranar Lahadi mai zuwa.
Jami'an masu matsakaicin shekaru 37, sun fito ne daga bangarori daban-daban na rundunar 'yan sanda, kana sun kware kan harsunan kasashen waje.
Tun bayan shiga shirin wanzar da zaman lafiya na MDD a shekarar 2000, kasar Sin ta tura jimilar jami'an 'yan sanda 2,614 ga shirye-shiryen wanzar da zaman lafiya 9 da kuma hedkwatar MDD dake birnin New York. A cewar ma'aikatar, jami'an sun samu kyakkyawar shaida a fadin duniya. (Fa'iza Mustapha)