Ma Zhaoxu, ya bayyana haka ne a jiya, yayin wata muhawara na kwamitin sulhu na majalisar kan hada hannun wajen daukar matakin inganta ayyukan shirye shiryen wanzar da zaman lafiya.
Ya ce ya na da matukar muhimmanci a inganta karfin kasashen dake bada gudunmuwar soji, musammam kasashe masu tasowa, tare da kara inganta hadin kai da kungiyoyin shiyya.
Da yake jadadda matsayin kasar Sin, wadda ita ce ta 2 wajen bada gudunmuwar dakaru cikin mambobin kwamitin, kuma ta 2 wajen bada gudumuwa mai tsoka ga kasafin kudin shirin wanzar da zaman lafiya, ya ce kasar Sin ta kafa rundunar sojin mai dakaru 8,000 dake jiran ko ta kwana, kuma tuni ta tura kashin farko na jiragenta masu saukar ungulu zuwa nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)