Abdeltif Loudyi, ministan kasar Morocco, da laftanal janar Carlos Humberto Loitey, mai bada shawara kan harkokin soji na shirin wanzar da zaman lafiya na MDD, sun kuma tattauna game da irin gudunmowar da Moroccon ke baiwa shirin na MDD.
Jami'an biyu, sun nazarci matakan da za'a bi wajen inganta shirin wanzar da zaman lafiyar na MDDr.
Game da wannan batu, Loudyi ya jaddada irin kokarin da masarautar Moroccon ke yi wajen samun nasarar shirin kiyayen zaman lafiya, kana ya yabawa sabbin dabarun da babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya bullo da su, a matsayin wasu sauye-sauye da za su taimakwa shirin kiyaye zaman lafiyar na MDDr.
Haka zalika, Loitey, ya jaddada ta'aziyya ga masarautar bisa rasuwar wasu jami'ai masu wanzar da zaman lafiyar 'yan kasar Morocco a lokacin da suke bakin aiki, bisa irin jarumtar da suka nuna a wajen aikin kiyaye zaman lafiya a jamhuriyar tsakiyar Afrika.(Ahmad Fagam)