Walikin musamman na magatakardan MDD Fareed Zarif, da wasu jami'an tawagar musamman na MDD dake kasar Liberia, da kuma wasu jami'an ofishin jakadancin kasar Sin dake kasar Liberia, da na gwamnatin kasar Liberia kimani mutane 50 suka halarci bikin.
A yayin bikin, Fareed Zarif ya bayyana cewa, kasar Sin, kasa ce dake kan gaba wajen tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa kasashen waje, lamarin da ya nuna cewa, kasar ta cika alkawarin da ta yi wa MDD, da ma sauran kasashen duniya ta fuskar wannan aiki. Haka kuma, ya nuna godiya matuka ga sojojin kiyaya zaman lafiyar kasar Sin bisa babbar gudummawa da suka bayar wajen kiyaye zaman lafiya a kasashen duniya. (Maryam)