Wakilin kasar Sin ya yi kira ga kasa da kasa da su daidaita matsalolin da ke jawo hankalin sassa daban daban a siyasance
Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD, Wu Haitao a jiya Laraba ya bayyana cewa, kamata ya yi kasa da kasa su daidaita matsalolin da ke gaban sassa daban daban a siyasance. Ban da wannan, ya kamata ayyukan kiyaye zaman lafiya na MDD su taimaka ga kokarin da ake yi, don samar da damar daidaita matsalolin a siyasance.
Ya ce, kasar Sin kasa ce da ke yawan tura sojojin masu kiyaye zaman lafiya, haka kuma ta zo ta biyu ta fannin zuba kudin kiyaye zaman lafiya. Kasar Sin tana son hada kan mambobin MDD, don kyautata tsarin aikin kiyaye zaman lafiya na MDD, da kiyaye zaman lafiya da tsaro a duniya. (Lubabatu)