in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Gambia ya gana da Wang Yi
2019-01-06 16:50:43 cri
Jiya Asabar, shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya gana da mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin waje Wang Yi a birnin Banjul, fadar mulkin kasar ta Gambia.

A yayin ganawar tasu, shugaba Barrow ya bayyana cewa, wannan shi ne karo na farko da ministan harkokin wajen kasar Sin ya kai ziyarar aiki a kasar Gambia, inda ya nuna fatan kasar Sin wajen raya dangantakar dake tsakaninta da kasar Gambia. Kuma ya taba kai ziyarar aiki sau biyu a kasar Sin cikin watanni 9 da suka gabata, lamarin da ya nuna cewa, shi da gwamnatin kasar Gambia suna mai da hankali sosai wajen karfafa dangantakar dake tsakanin kasar Gambia da kasar Sin. Kasar Sin aminiyar kasar Gambia ce, kasar Gambia tana sa ran karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu bisa bukatunta a fannin siyasa, kuma kasar tana fatan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu za ta ci gaba da bunkasa cikin yanayi mai kyau. Kasar Gambia tana tsayawa tsayin daka kan manufar "kasar Sin kasa daya tak a duniya", kana za ta ci gaba da goyon bayan kasar Sin cikin harkokin MDD da na kasa da kasa.

A nasa bangare kuma, Wang Yi ya ce, dangantakar dake tsakanin Sin da Gambia tana bunkasuwa cikin yanayi mai kyau bayan da kasashen biyu suka farfado da huldar diflomasiyya dake tsakaninsu. Kuma, farfadowar huldar diflomasiyya a tsakaninta da kasar Sin, wani kuduri daidaito ne da kasar Gambia ta yi, wanda ya biya bukatun gwamnati da al'ummomin kasarta, da kuma dacewa da halin da ake ciki yanzu a duniya. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China