in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)Sin ta mai da Afirka mihimmin matsayi cikin harkokin diflomsiyya, in ji Wang Yi
2019-01-04 11:02:51 cri
A jiya Alhamis ne mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin, kana ministan harkokin waje Wang Yi, ya gana da ministan harkokin wajen kasar Habasha Workneh Gebeyehu a birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasa ta Habasha. Bayan ganawar tasu, sun gana da 'yan jaridu cikin hadin gwiwa.

Wang Yi ya ce, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan fara ziyarar aiki a ko wace shekara a kasashen Afirka cikin shekaru 29 da suka gabata. Wannan ya kasance kyakkyawar al'adar gargajiya ta fuskar harkokin diflomasiyyar kasar Sin. Ya kuma nuna cewa, kasar Sin ta ci gaba da mai da kasashen Afirka wani muhimmin matsayi cikin harkokin diflomasiyyar ta. Kaza lika karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka da ma kasashe masu tasowa, shi ne babban burin kasar Sin kan aikin diflomasiyya.

Wang Yi ya ce, an cimma nasarar gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a watan Satumba na shekarar 2018. Kuma a wannan karo, ya kai ziyarar aiki a kasashen Afirka, domin aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron, ta yadda za a ci gaba da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, yayin da ake kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare.

Duk a wajen taron manema labaru da ya gudana a Addis Abeba, bayan ganawar ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi da takwaransa na kasar Habasha Workneh Gebeyehu. Cikin jawabinsa, Wang Yi ya gabatar da wani shiri mai taken "Shigewa gaba a fannoni guda uku". Da farko ya ce, ana fatan fahimtar juna tsakanin Sin da Habasha zai ci gaba da kasancewa a kan gaba. Kasashen biyu za su ci gaba da nuna goyon baya da fahimta ga juna kan manyan harkokin dake janyo hankulansu. Kuma kasar Sin tana tsayawa tsayin daka wajen ba da taimako ga kasar Habasha, don ta nemi wata hanyar neman ci gaba da za ta dace da halin da kasar take ciki, da kare mulkin kanta yadda ya kamata, da kuma raya tattalin arziki da zaman rayuwar al'ummar ta.

Sa'an nan kuma, Wang Yi ya ce, ana fatan Sin da Habasha za su kasance a sahun gaba a fannin aiwatar da shawarar "Ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa.

A karshe dai, ya ce, Sin na fatan Sin da Habasha za su zamo kan gaba a fannin yin hadin gwiwa ta fuskar harkokin kasa da kasa. Ya ce kasar Sin tana son yin mu'amala da kasar Habasha, a harkokin gyare-gyaren kwamitin sulhu na MDD, da sauyin yanayi, da jadawalin neman dauwamemmen ci gaba nan da shekarar 2030, da dai sauran harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya, ta yadda za a kiyaye moriyar kasashen biyu da ta sauran kasashe masu tasowa yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China