Wang Yi ya ce, ministan harkokin wajen kasar Sin ya kan fara ziyarar aiki a ko wace shekara a kasashen Afirka cikin shekaru 29 da suka gabata. Wannan ya kasance kyakkyawar al'adar gargajiya ta fuskar harkokin diflomasiyyar kasar Sin. Ya kuma nuna cewa, kasar Sin ta ci gaba da mai da kasashen Afirka wani muhimmin matsayi cikin harkokin diflomasiyyar ta. Kaza lika karfafa hadin gwiwar dake tsakaninta da kasashen Afirka da ma kasashe masu tasowa, shi ne babban burin kasar Sin kan aikin diflomasiyya.
Wang Yi ya ce, an cimma nasarar gudanar da taron dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka a watan Satumba na shekarar 2018. Kuma a wannan karo, ya kai ziyarar aiki a kasashen Afirka, domin aiwatar da sakamakon da aka cimma a yayin taron, ta yadda za a ci gaba da inganta dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka, yayin da ake kyautata dangantakar dake tsakanin Sin da Afirka bisa manyan tsare-tsare. (Maryam)