in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: tsayawa tsayin daka kan ka'idar Sin daya tak
2019-01-05 16:23:36 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya yi shawarwari tare da takwaran aikinsa na kasar Burkina Faso Alpha Barry, daga bisani kuma sun gana da 'yan jarida tare.

Wang Yi ya bayyana cewa, a watan Mayun shekarar bara, shugaban kasar Burkina Faso Christian Kaboré ya tsaida muhimmin kudurin mayar da dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasarsa da kasar Sin bayan shekaru 24 da suka gabata, kasarsa ta sake nuna amincewa ga ka'idar Sin daya tak, kuma an bude sabon babi na raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Wannan ne zabi mafi dacewa bisa daidaiton da kasa da kasa suka cimma da yanayin da ake ciki, babu shakka za a sa kaimi ga samun bunkasuwa mai dorewa a kasar Burkina Faso da kawo moriya ga jama'ar kasar gaba daya, da samar da dama wajen samun kyakkyawar makoma a wannan fanni.

Wang Yi ya bayyana cewa, shi da shugaba Kaboré da minista Barry sun cimma daidaito cewa, ka'idar Sin daya tak tushen siyasa ne ga raya dangantakar dake tsakanin Sin da Burkina Faso, tilas ne a tsaya tsayin daka kan ka'idar. Yin imani da juna shi ne tabbaci wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya kamata su ci gaba da nuna goyon baya ga juna kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu. Sassan biyu sun amince da tabbatar da matsaya guda da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da sakamakon da aka samu a gun taron koli na Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, da raya dangantakar abokantaka ta samun moriyar juna a tsakaninsu, da kara yin hadin gwiwa don amfanawa jama'arsu. Kana za a kara yin hadin gwiwa da mu'amala da juna kan harkokin kasa da kasa, da nuna goyon baya ga ra'ayin bangarori daban daban, da tabbatar da moriyar kasashe masu tasowa tare. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China