in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wang Yi: Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro a Afirka
2019-01-05 16:25:11 cri
Memban majalisar gudanarwar kasar Sin kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi da takwaran aikinsa na kasar Burkina Faso Alpha Barry sun gana da 'yan jarida tare bayan da suka yi shawarwari a ranar 4 ga wata.

Game da batun hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro, Wang Yi ya bayyana cewa, zaman lafiya yana da muhimmanci sosai ga nahiyar Afirka, shi ne tabbaci wajen raya Afirka. Sin ta yi kokarin samar da gudummawa ga Afirka, da taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka. Sin ta shiga-tsakani kan manyan batutuwan Afirka, ciki har da batun kasar Sudan ta Kudu, da nuna goyon baya ga ra'ayin 'yan Afirka su warware matsalolin Afirka ta hanyar Afirka. Sin ta nuna goyon baya ga MDD, ta gudanar da ayyukan kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka, ta zama kasa ta biyu wadda ta fi zuba jari ga aikin kiyaye zaman lafiya, kana ita ce kasar da ta fi tura ma'aikatan kiyaye zaman lafiya ga nahiyar Afirka a cikin kasashe 5 membobin kwamitin sulhun MDD na dindindin. A kwanakin baya, a matsayin kasar dake shugabancin kwamitin sulhun MDD a wannan karo, kasar Sin ta bukaci a gudanar da muhawarar ayyukan kiyaye zaman lafiya a nahiyar Afirka don sa kaimi ga kasa da kasa da su kara maida hankali ga batun kiyaye zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka.

Sin za ta ci gaba da maida hankali ga zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka, bisa buri da bukatun kasashen Afirka, Sin za ta kara yin kokari da samar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a nahiyar Afirka. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China